Wannan labari gaskiya ne. Najib ajib suna, na kasance mai - TopicsExpress



          

Wannan labari gaskiya ne. Najib ajib suna, na kasance mai matuqar son mata fiye da qima, idan budurwa taɗau wanka, ko mai kyau ko kishiyar haka, sukan ɗaɗani da qasa, a duk inda taron yan mata yake, sai naje, wajen walima, lonchon, fati, gidan biki, islamiya ta mata idan zaayi saukar quran, ko baa gaiyace ni ba, sai na halatta, domin kawai naga yan mata, idan kwa aka ce, ana wata sabga a unguwarmu, ta mata, ba inda nake zuwa, tun safe har sai taro ya watse. Zama kwa a bakin titi, domin yan mata masu giftawa, ya zamar min ruwan dare, a kwai lokacin da wata makaranta zata karrama ɗalibanta, daga inda nake zuwa makarantar matan tafiyar kilomita sha shida ne, amma rana tana buguna, haka nayi dagiya na tattaka, na isa dan bani da kudin bus, nasha zuwa jamioi gashi de ni ba ɗalibi ne ba, amma haka zan zauna, tun safe har yamma, ga yunwa, ga qishirwa amma haka zan jure, ina ganin adon-gari masu shigowa da ficewa, kuma duk hakan, abin baqin cikin bana iya yi musu magana, sai de na kalla kawai. Lokacin dana haɗu da sadiya ibrahim zango, sai abuwa suka chanja, na sota, kamar zan haɗiye ta, ita kuma data fahimci tsananin jarabar sonta , ya kamani, sai ta shiga wahala ni, na sha jar wahala akan sadiya zango, a qarshe, ba laifin kome ta wan wanka min mari, hagu da dama, a bainar jamaa maza da mata, a wajen wata walima da akayi, ta cicci min mutumchi, tun daga lokacin nasan mata sai a slow, allah na gode yanzu tsakanina da yan mata, sai de su wuce na wuce, in naga zasu bangaje nima, sai nai maza na basu hanya, in sun wuce naci gaba da tafiya. Wasu matan sukan ce namiji ba ɗan goyo bane, idan kunce haka, ku kuma ba, yan ɗauka bane da amincewa. Sadiya zango kin wahala ni, allah ya saka min, ina miki fatan ki haɗu da irin su dinasir, ehe! Ki gane kurenki. Jamilu zainab.
Posted on: Fri, 29 Nov 2013 20:42:43 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015