Wata kotu a kasar Nezaland ta yanke wa wani yaro dan shekara 15 - TopicsExpress



          

Wata kotu a kasar Nezaland ta yanke wa wani yaro dan shekara 15 daurin shekara saboda kisan gillar da ya yi wa wata yarinya ’yar shekara 15, sannan ya yi yunkurin halaka iyayenta, don kawai ana zarginta da tura wa wata yarinya kalaman kaskanci da cin mutunci ga wata yarinya a shafin sadarwar Facebook. Yaron dan shekara 15, mai suna Jin Hua K, an yanke masa hukuncin daurin shekara, sannan zai shafe shekara biyu a asibitin masu tabin hankali, saboda kisan gillar da aikata a ranar 14 ga Janairun bana, a gabashin birnin Arnhem. Wannan hukuncin da aka yanke shi ne mafi tsananin da aka taba yi wa karamin yaro a kasar Nezaland. “Kotu ta fahimci cewa wanda ake tuhuma da laifi ya yi kisan ne da gangan, ita yarinyar mai suna Joyce Hau, wadda kawayenta da abokai ke yi wa lakabin Winsie, sannan ya yi yunkurin halaka mahaifinta, a cewar alkali, a hukuncin da ya yanke da aka baza a shafin yanar sadarwa. Masu gabatar da kara, sun bayyana wa kotu cewa an yi kisan gillar ne, bayan Hau ta yi sa-in-sa a shafin facebook da wata kawarta ’yar shekara 16, wadda aka sani da sunansa Polly W. Saurayin Polly dan shekara 17 mai sunan Wesley C. ya shirya yadda aka aiwatar da kisan, don haka ya tuntubi Jing Hua K ta shafin Facebook, bayan ya shirya yadda za a kashe yarinyar, sai kuma ya tattauna da wasu kan yadda za a halaka iyayenta gaba daya. Jing Hua K. ya je gidan su Hau, inda ya bayyana mata cewa zai ba ta wani abu. Tana bude kofa, sai ya rika caka mata wuka, sannan ya kai wa babanta hari, inda ya soke shi a fuska, kamar yadda kotu ta saurari karar. “Da wuka ya soketa a wuya da fuska har ya kusan kasheta,” inji alkali. Nan aka bar yarinyar kwance cikin jini, ta kuma mutu a asibiti bayan kwana biyar. “Wanda ake tuhuma da laifi bai ma san insie ba, amma ya yi amfani da umarnin wani ko wasu,” kamar yadda aka bayyana a hukuncin da aka yanke. Wannan kara an yi ta takaddama akanta, har ta kai ga an yi mata lakabi a kasar Nezaland da sunan “Kisan Facebook.” Wanda ake tuhuma da laifin kisan babu sanayya a tsakaninsa da wadda ya kashe, amma an ba shi kwangilar kisan gillar ne a kan kudi Yuro dubu daya. Saurayi ya kashe tsohuwar budurwarsa da wanda ta aura Saurayin wata yarinya ya harzuka bayan an aurar da masoyiyarsa ga wani mutum, don haka ya kasheta tare da mutum hudu, sannan ya halaka kansa, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai ya ruwaito daga birnin New Delhi ta Indiya. Mutumin dan shekara 25, mai suna Rabi, ya harbi matar da sabon angonta da mai gidan hayarta, sannan ya tafi gidan iyayenta ya harbe babanta da ’yar uwarta, kamar yarda kafar sadarwar Indiya ta Trust of India ta bayyana. Rabi dai ya dade yana soyayya da tsohuwar budurwarsa, har ma da aurenta tsawon shekara guda, duk da haka yana cike da bakin ciki da takaicin iyayenta da suka hana shi aurenta, kamar yadda wani babban jami’in ’yan sanda ya bayyana. Dama al’adar kasar Indiya iyaye ke zaba wa ’ya’yansu abokan zaman aure, namiji a zabar masa mata ko mace a zabar mata miji, duk da cewa a halin yanzu an dan samu sauyi, inda wasu matasan ke yin auren soyayya. Mujallar The Times of India, ta ce Rabi ya samu wata ’yar karamar bindiga (pistol), da kuma wata babba mai dauke da dimbin harsashi. Saboda lasisi rike ko mallakar bindiga na da wuya a kasar, akwai masu cinikin makamai ba bisa ka’ida ba; wasu ma har kerawa suke yi. Don haka ake yawan samun bindigogi, kuma ake ganin wanda ya mallakesu tamkar ya samu wani matsayi a cikin al’umma. A lokacin da Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya tattara bayanai, mai amgana da yawun ’yan sanda baya nan ballantana ya yi bayani. ’Yar shekara 16 ta zama Magajiyar garin Allar da ke Falasdinu Bashaer Othman wata yarinya ’yar shekara 16 a garin Allar da ke Falasdinu, ta shae hutun makarantarta na wata biyu a matsayin Magajiyar garin Allar. Maimakon ta yi ta yawo da kawaye, sai ta hau kujerar magajin garinsu da ke Arewacin kogin Jordan. A ofishinta a kwai makeken tebur dauke da hotunanj Shugaba Mahmud Abbas da Firayiminista Slam Fayyad da kuma tsohon shugaban gwagwarmayar Falasdinawa, Yasser Arafat. Bashaer Othman tana cike da fara’a a yayin da take sanya hannu a kan takardar da za ta bai wa wani mazaunin garin dammar dimbin kudin ruwa day a taru a kansa. “Ba wai mukamin ne ya dame ni ba, a’a, bukatata in yi wa al’umma hidima a wannan gari,” inji wannan yarinya, wadda a lokacin da ta karbi ragamar mulki daga hannun Magajin gari Sufiyan Shadid, a ranar 2 ga watabn Yulion bana, tana ’yar shekara 15. Mazauna garin Allar sun kai mutum dubu takwas. Kuma manufar bat a wannan mulki, shi ne a koya wa matasa yadda ake gudanar da harkokin mulki, kamar yadda wata kungiyar matasa ta Sharek Youth Forum ta tsara, wato yara matasa su rika shiga ana damawa da su a harkokin gwamnatin kananan hukumomi a Falasdinu. Wani ya yi caca da jarin kasuwancin hadin gwiwa har Naira miliyanN254 da dubu400 Wani mai saka hannun jari a Indiya ya yi caca da kudin abokin kasuwancinsa Dala 92,500, abokiyar hadin gwiwarsa Misis Liu guiling ta mika masa kudin, don sayi kantinm hada-hadar kasuwanci a wani gari da ake kira Little India’ as cikin watan Afrilun bara. An tsara yadda abokin kasuwancinta, Tan Kah Hock zai adana musu kudinsu a bankin Standard Chartered, tare da hannun jarinsa na Dala miliyan daya da rabi. Maimakon ya zuba kudin a bankin, sai kawai ya tafi gidan caca na Sentosa (World Sentosa Casino) ya rika buga caca a kullum; kudin da ya salwantar a wajen caca sun kai Naira miliyan 254 da dubu 400 a kudin Najeriya. Tan dan shekara 62 kotu ta yanke masa daurin shekara da wata bakwai.
Posted on: Tue, 02 Jul 2013 19:49:08 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015