Wata rana naje, wani ƙauye ziyara, aka nuna min ɗakin da zan - TopicsExpress



          

Wata rana naje, wani ƙauye ziyara, aka nuna min ɗakin da zan kwana, aka ce mini, sai nayi hakuri, domin abokin kwanana, wani lokaci yana zarewa. Tsakar dare, na kwanta, kwatsam sai naji ana buɗe ƙofa, sai naji mutum sai suraitai yake yi, ɗan jimawa yai shuru. Sai naji antaɓa ni, waye wannan? nace masa nine. Oh kaine madallah ɗan jimawa kaɗan ya kuma taɓa ƙugunawai waye wannan? nace masa nine, yayi shuru, ɗan jimawa, ya taɓa cinyata waye ne? nine na amsa. Oh duk kaine? jimawa can ya kuma taɓa ƙafafu na waye wannan? na amsa da nine. Sai yace daman na sayo sabuwar takobi a kasuwa yau, gaskiya kayi tsayi sai na rage ka, tsayin naka yai yawa jamilu zainab.
Posted on: Sat, 09 Nov 2013 20:45:28 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015