YANA JIRAN AYA KO HADISI KAFIN YA KARBI ILIMI Via:Rayuwar - TopicsExpress



          

YANA JIRAN AYA KO HADISI KAFIN YA KARBI ILIMI Via:Rayuwar Matasa a Yau Like:Rayuwar Matasa a Yau Abin ba zai baka mamaki ba idan ka yi maganar da ilimi da bincike suka tabbatar wani ya tambaye ka ina aya ko hadisi? Manzon Allah SAW wata rana ya wuce wadansu mutane suna yiwa dabino kilili (barbara) sai ya tambayesu me yasa suke yin haka sai suka ce su na yi ne domin ya fitar da dabino masu yawa. Sai Maaiki SAW ya ce ai da ma baku yi haka ba da ya yi. A wannan shekarar sai Dabino ya yi wabi, sai Manzon Allah ya ce ya aka yi wannan shekarar ba a samu Dadibo ba sai suka ce ya Manzon Allah mun yi amfani da maganar ka ne shi yasa ba mu yi ba kilili ba. Sai Manzon Allah SAW ya ce: Ku kuka fini sanin alamarin duniyar ku. Lokacin da aka je yakin Badar sai Manzon Allah ya sa aka saka ruwa a gaba, wani daga cikin sahabbansa (Allah ya yarda dasu duka) ya ce, tsayawar da muka yi a wannan wuri, umarnin Allah ne, ko kuma kai kaga ya dace da mu tsaya. Manzon Allah (SAW) ya ce: Ina ganin kamar haka ya dace sai wannan sahabi nasa ya ce: A harkar ya ki, ana saka ruwa ne a baya idan makiya sun taho za su yi kokarin neman sa mu kuma sai mu far masu. Dukkan wadansu abubuwa da muke gani a yanzu, wadanda suka shafi, Kimiyya da Fasaha ta kowane bangare tana tabbatar da annabcin Manzon Allah ne. Muna da misalai da yawa! Saboda haka abin ya bamu mamaki mun fadi irin binciken da aka yi na irin bayanai da karamar kwakwalwa za ta iya dauka, wanda tun daga lokacin da mutum yayi wayo, kwakwalwarsa ta ke dauke da bayanai, duk wanda aka ce yanzu za a fito masa da bayanai da kwakwalwarsa ta rike ko ta sani, kamar yadda ake saka su a cikin kwamfuta ina tabbatar muku da cewar ta fi karfin exabyte 256. Mutane da yawa kullum burinsu, idan aka ce ga wani abu na rayuwa abin da suke nema shine a kawo aya ko hadisi tukun kafin su yi aiki da shi. To wallahi ina tabbatar muku irin wadannan mutane ko da aya ko hadisi aka kawo musu ba za su yi imani ba. Allah ma da kansa ya fadi haka. Irin wadannan ilmoma da ake yawan fadawa mutane ba wai maganar Sallah ba ce, ko azumi, ko zakka ko aikin hajji ba ne, ko muamala da dai makamantan abin da addini ya ce ayi ko a bari. Ba kuma wannan ilimin haramtawa ba ne ko halastawa, a a ana kiyasta irin kudura da irada da Allah ya ke da ita da kuma baiwar da ya yiwa dan adam. Kai dan uwa! ka dawo hayyacinka, ka fahimci cewar shayi ruwa ne, ka gane cewar ilimin da Allah ya baiwa alummar Annabi Muhammad SAW ya wuce da sanin ka! Via:Rayuwar Matasa a Yau Like:Rayuwar Matasa a Yau Admin Auwal Bauchi
Posted on: Wed, 30 Oct 2013 06:42:55 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015