Ya ‘yan uwana, kamar yadda Allah ya bamu labari acikin al-qurani - TopicsExpress



          

Ya ‘yan uwana, kamar yadda Allah ya bamu labari acikin al-qurani mai tsarki; wannan wata da yake tun karomu na Ramadhan shi ne watan alqurani kamar yadda Allah ya shaida mana a cikin sura ta 2 aya ta 185, Allah ta’ala da kanSa ya yi kira a garemu cikin wannan aya da cewa duk wanda ya halarci wannan wata ma’ana duk wanda ya riski kansa a wannan lokaci to ya azumceshi. Haka kuma har ila yau Allah ya cigaba da shaidamana acikin wannan sura aya ta 183 cewa shi wannan wata kwanaki ne kididdigaggu, kamar Allah yana cewa ne muyi amfani da lokutanmu ta hanyoyin da suka dace a cikin wannan wata
Posted on: Sat, 29 Jun 2013 10:18:58 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015