#ZABEN_ANAMBRA: Game Da Sakamakon Zaben Jihar Har zuwa yanzu - TopicsExpress



          

#ZABEN_ANAMBRA: Game Da Sakamakon Zaben Jihar Har zuwa yanzu hukumar zabe (INEC) ba ta bayyana wanda ya samu nasarar lashe zaben Anambra ba, saboda a cewar hukumar adadin kuriun da aka soke sun zarta adadin tazarar da jamiyyar #APGA dake kan gaba ta yi wa #PDP wadda take biye da ita, kamar yadda INEC din ta bayyana a safiyar yau da misalin 6:50am. Sannan kwamishinan zaben jihar ya bayyana cewa ba za a san wanda yayi nasarar lashe zaben ba har sai an sake yin wani zaben a wasu yankunan da aka samu kuriun da aka soke masu yawa. Yadda sakamakon zaben yake kamar yadda INEC din ta bayyana, a cikin kananan hukumomi 21, dan takarar APGA, Willie Obiano, yayi nasara a 16. Kwamrad Tony Nwoye na PDP da Chris Ngige na APC duk sun yi nasara a kananan hukumomi bi-biyu, sai kuma Dr. Ifeanyi Ubah na LP da ya samu nasara a karamar hukumarsa kadai. #RARIYA za ta kawo muku yadda lissafin adadin kuriun da kowane dan takara ya samu.
Posted on: Mon, 18 Nov 2013 08:12:53 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015