ZAKKAR KONO ( FIDDA- KAI ): a – HIKIMAR SHAR’ANTATA: An - TopicsExpress



          

ZAKKAR KONO ( FIDDA- KAI ): a – HIKIMAR SHAR’ANTATA: An shar’anta zakkar kono ne domin tsarkake mai azumi daga maganganun banza da kwarkwasa, domin kuma ciyar da miskinai da wadatar da su ga barin roko a ranar salla. Dalili a kan haka hadisin Ibnu Abbas Allah ya yarda da su ya ce: “Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya farlanta zakkar buda baki domin tsarkake mai azumi daga maganganun banza da kwarkwasa, domin kuma ciyar da miskinai” Abu Dawud ne da Ibnu Majah suka ruwaito shi. b – HUKUNCINTA: Zakkar kono farillace a kan kowane musulmi da musulma, babba da karami, Da da bawa; dalilin haka hadisin Ibnu Umar Allah ya yarda da su ya ce: “ManzonAllah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya farlanta zakkar buda baki na azumin ramadana sa’i na dabino, ko sa’i na sha’ir, a kan bawa da Da, na miji da mace, karami da babba daga cikin musulmi, ya kuma umartci a fitar da zakkar kafin mutane su fita salla” Bukhari da muslim ne suka ruwaito shi. Kuma ana so a fitar da ita a madadin Dan tayi. Wajibi ne kuma musulmi ya fitar da ita a madadin kansa da wadanda ciyar da su take kansa, kamar matarsa da danginsa makusanta. Zakkar kono ba ta wajaba sai a kan wanda ya mallaki fiye da abin da zai ciyar da kansa da iyalansa a ranar salla da darenta.
Posted on: Fri, 02 Aug 2013 14:39:53 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015