ZUWAN MAI MALFA, A SOKOTO A ja jibirin ranarda Mai Malfa zai zo - TopicsExpress



          

ZUWAN MAI MALFA, A SOKOTO A ja jibirin ranarda Mai Malfa zai zo Sokoto tun lokacin Jamian tsaro ke kama ta musgunawa tare da tozartawa alumma, wai don Shugaban kasa zaizo. Wannan yasa na tuna a 2002 lokacinda shugaban kasa Chief Oleshegon Obasanjo yattafo Sokoto, tun daga baki Makarantar Sheikh Abubakar Gummi mutane ne jejjere, suna yiwa shugaban kasa Marhabin lale da zuwa Sokoto, wanda har yayi sanadiyyarda aka bashi wata Sarauta awaccan lokaci. Amma kash! Wai sai gashi yau Ebola yazo Sokoto tun daga bakin Filin jirgi alumma ke kama tofin Allah tsine, suna kuma nuna cewa mu kam bamu ba kai, Genaral Muhammadu Buhari mukeso. Domin ya fitardamu daga cikin kunci da mawuyacin hali da kassanyamu acikinsa. Awasu wurare ma, mun samu rahoton cewa har kuwwa akayi masa shida tawagarsa, awata unguwa kuma har jefar Tawagarsa akayi. Wannan shi ya nunawa Duniya cewa mu kam Sakkwatawa ko da alama bamu tare da wanda bai iya Mulki ba, kana kuma baima san yadda ake Mulki ba, Illa hanyarda yassani kadai itace, ta yaya zaa danfari alumma ta yaya zaa sace musu arziki, ta yaya zamu arzurta kawunanmu, ta yaya zamu jefa musu Talauci kana da kuma fatara d.s. Wani abin ban dariya kuma shine irin yadda sukayi taronsu a filin sukuwa, dukkaninsu manyan jagororin tafiyar ba mai akalla mutum 15 a runfunansu, balle har su iya taka wata rawar azo agani alokacin zabe. Duk wanda yagga taronku a NTA yasan baku samu yadda kuke so ba, dukda da makuddan kudadenda aka kashe wajen gayyato talakawa domin su kashe muku kunya. Kuzo ranar Alhamis 22/01/2015 kuga taronda Ba kudi, ba tilastawa, ba cin zarafin alumma ba musgunawa alumma, ba tareda ko sisin kwaboba, kaga mutum ya kashe kasuwancinsa, ya dakatarda Nomansa, ya dakatarda duk aikinda yake yazo yaga kana kuma yaji jawabin Mai gaskiya kana da rikon amana waton shine General Buhari bakin cikin Yan Jonatanism. YA ALLAH DON SUNAYENDA 99, WADANDA KACCE DUK WANDA YARROKEKA DASU ZAKA KARBA MASA, YA ALLAH KA BAIWA GENERAL BUHARI MULKIN NIGERIA A 2015. YA ALLAH KA BAIWA RT. AMINU WAZIRI TAMBUWAL GWAMNAN JAHAR SOKOTO A 2015, YA ALLAH KA BAIWA ALU SARKIN YAMMA SANATAN SOKOTO TA TSAKIYA A 2015. YA ALLAH BAMUDA KARFI SAI NA DAGGA GAREKA. YA ALLAH BAMU DA DUBARA SAI DAGGA GAREKA. YA ALLAH BAMU DA IKO SAI NA DAGGA GAREKA. YA ALLAH KA IYAMUNA KA KUMA KARA YI MUNA JAGORA.
Posted on: Mon, 19 Jan 2015 19:00:25 +0000

Recently Viewed Topics




© 2015