Zabe na kasa ya soma kunno kai. Yan majalisarmu na tarayya (NASS - TopicsExpress



          

Zabe na kasa ya soma kunno kai. Yan majalisarmu na tarayya (NASS members) sun fara kawo jiki don bukatar kuriun bayin Allah Sakkwatawa. Kasan tun da suka shiga majalisa ai sun buya domin ko yan guntayen ayukan da suke hankoron sun yi, ba su ne ke zuwa budewa ba. Sai su turo yaran su. In har sun shigo birnin Shehu to sai wanda suka so gani zasu gani domin galibinsu a otel suke sauka. Galibinsu sun je majalisa sau 2,3 kai ga zahiri ma baa rasa mai 4th term. Muna ganin abinda NASS members na jihohin nesa kai har da ma na makwabtan mu irin Zamfara ke yi. Tau zabi ya rage ma Sakkwatawa cewa a yi siyasar akida. A yi siyasar mutum ba siyasar jamiyya ba.
Posted on: Sat, 09 Nov 2013 12:38:31 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015