kila gobe daren sallah. Assalamu alaikum ina mai bayyana godiya - TopicsExpress



          

kila gobe daren sallah. Assalamu alaikum ina mai bayyana godiya ta ga Mahallicina da Ya kaddara mani kaiwa wannan lokaci duk da cewa ina mai bakin cikin rabuwa da wannan makaranta da nake ciki wato RAMADAN amma kuma dole dalibi yayi farin cikin gama zangon karatu lafiya koda baisan abinda zai iske a wajen wannan makaranta ba. Akwai tarin abubuwan da ba zan manta da su ba a irin wannan rana ta daren sallah, amma bazan ambatawa mai karatu ko daya ba sai dai zan saki wani ARASHI wanda na san wasu zasu gane inda aka kwana wato ince DUK WANDA YAKE MURNA DA BANA TO BARA YA SHA WUYA. Karwanda ya tambaye ni mi yassa nace haka kai dai kawai kayi addua kar ka zamo yadda na zamo bara war haka.
Posted on: Mon, 05 Aug 2013 06:16:04 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015