¤ASHE HAKA YAN ALJANNA ZASU KASANCE???¤ An karbo daga Abu - TopicsExpress



          

¤ASHE HAKA YAN ALJANNA ZASU KASANCE???¤ An karbo daga Abu saidul khudiri (R.A) da Abu Huraira (R.A) daga Manzon Allah (s.a.w) Ya ce; mai kira zai yi kira a ranar alqiyama, ya ce Ya Ku yan Aljanna! Haka zaku dawwama a cikin Qoshin lafiya, babu cuta har abada, kuma za ku dawwama a cikin rayuwa babu mutuwa har abada, za Ku dawwama a cikin Quruciya babu tsufa har abada. Kuma za Ku dawwama a cikin Niima babu talauci har wbada. ALLHU AKHBAR! Wannan ya yi daidai da dadin Allah Madaukakin Sarki cewa; ( kuma a ka kira yan Aljanna a ka ce da su wannan gidan Aljanna ne, an gadar maku da ita sakamakon abin da Ku ka kasance Ku na aikatawa) Ya Allah ka niimta mu da niimar Ka. Ya Allah ka yi mana gafara domin kai mai gafartawa ne. Ya Allah Ka azurta mu duniya da lahira, don kai ne mai azurtawa. Ya Allah Ka sanya Mu a Aljanna don Rahmar Ka da daukakar Ka. Barkan Mu Da Jumaa
Posted on: Fri, 29 Nov 2013 08:27:54 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015