CIKAKKEN TAWAKKALI An tambayi Hatim Al-asamm akan me ka gina - TopicsExpress



          

CIKAKKEN TAWAKKALI An tambayi Hatim Al-asamm akan me ka gina alamarinka na dogaro ga Allah, sai ya ce : NA GINA SHI AKAN TURAKU GUDA HUDU : 1. Lokacin da Na san arzikina ba wanda zai ci don haka sai zuciyata ta nutsu. 2. Lokacin da Na san ba wanda zai yi min aikina, don haka, sai na shagala da shi. 3. Lokacin da Na san mutuwa za ta iya zuwa min a kowanne lokacin, sai na yi ta kokarin kusantarta. 4. Lokacin da Na san ko ina na shiga Allah yana gani na, sai nake jin kunyarsa. INA MA DA ZA MU GINA LAMURANMU AKAN WADANNAN TURAKU GUDA HUDU, DA KOWA YA HUTA DA HAWAN JINI, DA BUGAWAR ZUCIYA By Jamilu Zarewa
Posted on: Wed, 04 Dec 2013 20:35:25 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015