DAGA TASKAR FADAR BEGE.. Allahu sarki ka kaddara saduwa ta, Da - TopicsExpress



          

DAGA TASKAR FADAR BEGE.. Allahu sarki ka kaddara saduwa ta, Da Annabi tsaftatacce gadarar rayuwa ta, Ka yi min dan Maaiki dalilin samuwata. Allahu dado kusanci gurin rahamar halittu, Abin son masu ruhi abin neman matattu, Ka so shi ka samu komai a take a gun ka yan tu, Ka zama dan gidan sa hakika mun wadatu. Ya rahama ga kowa Maaiki kai na zaba, Allah kai ya zaba idan ka fada ya kar ba, Ta kai Manzo nake yi ka zaban kai na zaba, daga kai babu kowa Ilahu ba zai kuma ba. Annabi na biyo ka, dalili kai nike so. Mai maana cikakke, TaAla kai ya ke so. In ka so ya ce eh hakika ni ina so. Ya Maaiki ka so mu, mu kare mui ta na so. Nan ne zan takaita hadiya gun ki Nana, Uwar gida gun maaiki salamu alaiki Nana, Na zo ga ni da sallama gun ki Nana, A karban dan Maaiki mabudin samuwata. Kyakykyawa maaiki fiyayyen masu girma, mai daraja isashshe abin so Annabi na. Allahu Akbar Fadar Bege! Allah ka kyauta namu zuwan. via rayuwar duniya
Posted on: Sat, 19 Oct 2013 05:43:52 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015