Musulunci Hanyar Rayuwa KU BAYAR DA AMANA ZUWA GA MASU ITA Ahmad - TopicsExpress



          

Musulunci Hanyar Rayuwa KU BAYAR DA AMANA ZUWA GA MASU ITA Ahmad bn salman AnnajJad ya ce: "wata rana na shiga kunci mai tsanani da talauci, kwatsam ina cikin tafiya akan hanya sai na ci karo da wata tsohuwa sai ta ce: ya Ahmad ya na ganka kamar wanda yake cikin damuwa? sai na ce ki bari kawai! lamarin sai dai godiyar Allah! na dan tsinta mata halin da nake ciki. Sai ta ce: Kafin mahaifiyarka ta rasu akwai kudi da ta bani dirhami dari uku ta ce: ki boye wannan kudin, sai yayin da kika ga dana Ahmad yana cikin matsala da damuwa ta rashi sannan ki bashi, don haka sai ka zo muje gidana ka karbi kudinka. Allahu akbar! ka ga masu rikon amana na hakika. - A CIKIN WANNAN KO AKWAI ABIN KOYI GA MAI IMANI DA HANKALI?? - WA ZAI IYA FITAR MANA DA WATA FA`IDA DAGA CIKIN WANNAN KISSAR BANDA RIKON AMANA.
Posted on: Wed, 18 Sep 2013 20:34:40 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015