SALATI GA MANZON ALLAH (SAW) * ALLAH (SWT) yace: Hakika ALLAH da - TopicsExpress



          

SALATI GA MANZON ALLAH (SAW) * ALLAH (SWT) yace: Hakika ALLAH da Malaikunsa suna yin salati ga Annabi. Yaku da kuka yi imani! Kuyi salati a gare shi, kuma kuyi sallama domin amintarwa a gare shi (suratul Ahzab) * Manzon ALLAH (SAW) yace: wanda yayi salati daya a gare ni,to ALLAH zaiyi salati goma a gare shi (Muslim) * Manzon ALLAH (SAW) Yace: Mafifitan mutane ranar alqiyama gare ni, sune wadanda suka fi yi mini salati (Tirmizi) * ALLAH wadai da mutumin da aka ambace ni a gabansa amma bai yi min salati ba (Tirmizi) * Manzon ALLAH (SAW) Yace: ALLAH yana da wadansu malaiku matafiya a bayan kasa, suna isar min da sallama daga alummata * Manzon ALLAH (SAW) yace: Babu wani wanda zai yi mini sallama face ALLAH ya dawo min da raina na amsa masa sallamarsa *Manzon ALLAH(SAW) yace: kada ku maida kabarina kamar wurin idi, kuyi salati a gare ni ko ina kuke, domin salatinku yana isa zuwa gare ni (Abu dawud) ALLAH ya kara mana son Annabi (SAW)...Ameen Thumma Ameen.
Posted on: Fri, 29 Nov 2013 09:02:31 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015