SIFFAR BARCIN MANZON ALLAH SALLALLAHU ALAIHI WASALLALAM Ya kasance - TopicsExpress



          

SIFFAR BARCIN MANZON ALLAH SALLALLAHU ALAIHI WASALLALAM Ya kasance yana Barci a Farkon dare, ya raya karshensa – wato yanayin Sallah a cikinsa kenan- Bukharida Muslim. Ø Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam Ya Kasance idan ya hau kan shinfidarsa zeyi Barci yana cewa : “ Bismikallahumma Amutu Wa’ahyaa” (Ma’ana Da sunanka Ubangiji, nake Mutuwa kuma nake Rayuwa. Mutuwa = Yinbarci, Rayuwa = Farkawa daga barci) kuma idan ya farka daga barci yana cewa “ Alhamdu lil lahil ladhi Ahyaana ba’ada ma Amaatana Wa ilaihin nushur” ( Ma’ana Dukkan godiyata tabbata ga Allah Wanda ya Rayamu bayan ya kashe mu, kuma gareshi tashi yake) Muslim. Ø Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Ya Kasance idan ze kwanta barci yana sanya tafin Hannunsa na dama kar-kashin kuncinsa na dama se Yace: “Rabbi Qini azabaka Yauma tab’athu ibadika” (Ma’ana Ya ubangiji ka tsareni daga Azabarka ranar da zaka tashi bayinka –wato ranar Lahira kenan) Tirmidhi. Ø Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam Ya Kasance a kowani dare idan ze kwanta yana hada tafukan Hannayensa se ya huresu Ya karanta (Kulhuwallahu Ahad) da (Kul’a’uzu birabbil Falaq) da (Kul’a’uzu bi rabbin Nas), sannan yashafama inda ya sauwaka a jikinsa, yana farawa da kansa se fuskarsa da barin gaba na jikinsa, yana yin hakan sau uku. Bukhari da Muslim. Ø Ya Kasance yana barci a kan matashin kai (pillow) na Fata cikinsa an cikashi da gashin bishiyar dabino Ahmad. Ø Shimfidar da Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Ya Kasance yana barci akanta ta Fata ce da aka cika da gashin bishiyar dabino Muslim. Ø Nana Aisha Allah ya kara Yarda agareta tace Ya Manzan Allah Shin kana barci ne kafin kayi Sallar Witri?Se Yace: “ Yake Aisha: Idanuwana suna Barci amma Zuciya ta bata Barci” Bukhari da Muslim. Allah Ya Bamu Ikon Koyi Da Manzon Allah S.a.w.Ameen. Gud nyt. #Alkamawa!
Posted on: Sat, 28 Sep 2013 00:16:55 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015