WADANCAN MUTANEN BASU DA ALKIBLA Ba kune kuke fadawa mutanen - TopicsExpress



          

WADANCAN MUTANEN BASU DA ALKIBLA Ba kune kuke fadawa mutanen kano cewa ku yan rajin raya kasane ba? Kunce ku ba yan ci da addini bane, baruwanku da gyaran zukata, baruwanku da maganar daidaita sahu. Kunedai kuka turo jamian tsaro suka kame shugabannin HISBA da sunan yan taadda, hakanan kuka sawa Obasanjo sunan UBA SURAJO shikuma Jonathan kuka kirashi MAI NASARA duk da sunan mutanenmu su jefa musu kuria. Yanzu wanccan malamin gwamna daya assasa daidaita sahu, sharia, hisba, zakka, ciyarwa lokacin azumi, taimakon marayu, gajiyayyu, nakasassu da Islamic centre a kananan hukumomi 44 wai aganinku shine kuke kafirtawa? Duk dacewa kune ke dakile duk wani taimakawa addinin Allah daya gabatar a gwamnatinsa. Abin kunya kune ke fitowa kafafan yada labaru kuna kiran mutane suyi register domin zabenku? Bayan kun kori nakasassu daga gidajensu, kun rushewa bayin Allah gidajensu, kun daure shugabannin hisba, kun hana ciyarwa lokacin azumi, kun hana taimakon marayu, kun hana taimakon marasa lfy da basuda karfin sayen magani, duk wani balaii daya samu a kano baku taba jajantawa alummah ba. Kai, koma yan siyasar taku babu wanda kuka taimakawa, saboda kunki zaben kananan hukumomi wadanda sune sukafi kusa da jamaa, ballantana susa rai da kwalbatoci, gyaran magudanun ruwa ko gyaran makabartu ko zuba burji a titunansu.....indai wannan itace siyasar da kuke kira ayi register domin zabenku, toh gakunan ga jamaa.
Posted on: Sun, 09 Feb 2014 16:38:10 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015