Wasu Hadejawa ne su biyu suna tafiya zuwa wani gari, sai - TopicsExpress



          

Wasu Hadejawa ne su biyu suna tafiya zuwa wani gari, sai guzurinsu ya kare, ga yunwa kuma ta kama su. Guda daya ya ce shi zai je wurin mai fura, domin a yi masa damu. dayan kuma ya ce shi babu ruwansa da rigima. Bahadejen daya sai ya tafi wajen mai fura ya ce a yi masa damu, bayan an dama sai ya koma gefe daya cikin rumfa ya fara sha. Da ya kare sai ya rage ’yar kadan a kwaryar, ya zuba wa kansa ita kamar mahaukaci, ya ci gaba da surutai irin na tababbu shi kadai yana ta dariya. Da mai fura ta ga haka sai ta ce: “Ashe yau mahaukaci na sayar wa fura, to Allah sa kada ya fasa mini koko, asarar ta yi mini yawa. Can sai ya mike ya kwada ihu, ya fasa da gudu.
Posted on: Thu, 24 Oct 2013 14:11:54 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015