Wato duk wanda Allah ya daukaka dole yayi haquri da - TopicsExpress



          

Wato duk wanda Allah ya daukaka dole yayi haquri da MAHASSADA! Wani tare dashi kuke amma kuma hassadar ka yakeyi,, da yawa wasu suna nuna maka soyayya a fili amma kuma a zuciyar su suna Hassadar daukakar da ka samu! Kuma fah daukakar nan mutum bai isa ya bawa kansa ba,, Allah yake bayarwa... Don haka kai wanda ake hassada ka godewa Allah. Domin abun asali ya samo tun daga kan ANNABI ADAM AS!! Sai dai ka nemi tsari daga garesu a gurin ALLAH,,,,,, domin mai hassada ba qaramin masharranci bane, kuma wallahi komai zai iya yimaka!!! Ya Allah kayi muna tsari dasu...... Ameen!!!
Posted on: Sat, 20 Jul 2013 08:42:45 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015