Ya Ya Zanyi II? Ihun magoya bayan kwallon qafa ne ya batan min - TopicsExpress



          

Ya Ya Zanyi II? Ihun magoya bayan kwallon qafa ne ya batan min rai sakamakon murna da suke a lokacin da suka zura kwalo ta biyu a raga abokanan karawarsu inda nake goyan baya, bacin ran cin kwalon yasa na sanya hannuna a aljifu na fiddo da wayyata kona rage haushi, ga mamaki sai nai arba da miss calls guda 4 na mutum guda, Allah sarki Zubaida ban kirata ba ta kirani na fada a zuciya ta. Bayan an tashi daga wasa akan hanyata ta komawa gida na kira lambarta nai rashin dace wayar akashe take; Misalin 11pm naji ana kira wayana da yake ear piece ne a kunnena na amsa kiran da fadin hello, au Assalam Alaikum, aka amsa sallama akace dani kana magana ne da zubaida, nai murmushi nace sannu zubaida, ya kike ya gida? Tace dani Komai Fine, dama na kiraka ne don naga kwanaki biyu sun cika amma banjika ba, ina fata dai lafiya, nace da ita lafiya lau, kinsan yara irin mu in aka zo mana da abinda yafi kanmu sai mun danyi nazari kafin mu bada amsa, tai daria tace dani SO ya kake gani, ya ya? zamu iya haduwar, dan na tabbata kaima zata zama alfanu a gareka, in har ka yarda mai zai hana gobe Alhamis mu hadu, na baka dama duk inda kake gani yafi safe wajenka ka fadamin, sai da safe, ta kashe wayar kafin na maida amsa. Ranar Alhamis da yamma ina zaune a Yahuza Suya dake Alue Avenue ni dai ba kudin lemo gareni ba ballantana kudin sayan kaza, sai yaqe nake ina kallon talabijin din dake manne a bagon dakin, bugar teburin dake kusani ya sani waigawa, fuskar baiwar Allah mai sanye da glass din nan na qara arangama da ita, ta zauna kan kujera tayi min salama ta zuba min na mujiya da tabaran dake fuskarta, ta sanya hannunta ta cire glass din ta zaro wani gida mai kallar madara ta saka ciki. Ta kara kallata tana wani irin murmushi irin da yayan masu dashi tare da fadin sannu Ahmad, ina fatan ban batama rai ba dan nasan ka jima, wallahi nima akasi ak samu, nace da ita ba komi; karki damu, ki godewa Allah dana samu damar zuwa, dan ni kaina banyi tunanin zan iya ba amma zuciyata ta rinjayo ni, ina adduar abinda zaki fadan ya zama mai tushe, makama da alfanu. Sunana Zubaida kamar yadda na fadama ranar litinin, kusan shekara 4 da suka wuce na karanta wani labarinka amma na manta ko a jarida ko mujallar na gani, na kuma manta taken sunan labarin saboda ya jima, tun a lokacin na kiraka na tambayeka gaskiya labarin, ka ban amsa da cewa kirkiraran labari ne, amsar daka ban taban mamaki kasancewar kwata-kwata labarin bai kama da kirkirarai ba, tun a lokacin naso mu hadu dakai dan ina son in rokeka wani abu kuma nasan baza ka ki ba, nayi iyakacin iyawa dan mu hadu na ganka amma haqar daqi cimma ruwa, har nazo na rasa lambar layin ka, a sibili da haka yasa na koma nemanka ta social network na kuma ringa bibiyarka a haka har na tabbata zan iya shaidaka shi yasa ranar Litinin dana ganka da karfina na tsaya naima magana dan nasan kaine, amma abinda na keso gareka shine, wannan kazar da akawo muci in mun gama sai na fadama. Na yagi naman kaza na kora da lemo, na kama cin kaza ina shan lemo kai kace da kudina na saya, karar taken kasar najeriya yasa da sanya hanu a aljifuna ta zaro wayar na duba naga Mama ke kira, na latsa abin amsa kira, Ahmad kana ina ne, kayi ma za kazo yanzu, jikina ne ya mutu tare da fadin Mama ina alue avenue kafin na qara magana akace dani Dan Allah kai ma za kazo gida ina jiranka, nace to Mama gani nan zuwa insha Allah. Na kalli zubaida nace da ita, yanzu ya zamuyi a na nemana a gira Urgentlly, tace min ba komai muje nayi dropping dinka, mu hadu weekend sai na fadama amma fa ka kirani pls kafin lokacin, ba karamin ganganci nayi ba nace a raina yayin da take kokarin tsayawa da mota a inda nace zan sauka maana kofar gidan mu, har zan bude kofa na fita tace dani tana dariya; a gaskiya abinda zan fada ma yana da tsawo kuma na ga har yanzu baka gama amincewa dani ba, dan haka zan baka Weekends (asabar ko lahadi) duk abinda kaga zuciyarka tafi kwanta ma kana da lambar wayana ka kirani duk inda kake sai mu hadu! Na bude gate na shiga gida ina zancen zuci! Kai yan uwa har yanzu shawarku nake nema? dan ina son mu hadu weekend din ina kuma tsoron mu hadun!
Posted on: Fri, 08 Nov 2013 20:57:13 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015