ZAMA TARE DA MASU AMBATON ALLAH Manzon Allah s.a.w ya ba mu - TopicsExpress



          

ZAMA TARE DA MASU AMBATON ALLAH Manzon Allah s.a.w ya ba mu labarin cewa Lallai Allah yana da wasu Malaiku da suke ya wo adoron kasa suna neman Mutanen dake ambaton Allah (Karatun Alquran, waazi, tasbihi har ma tinatarda juna irin wannan) idan suka samu inda ake ambaton Allah sai suita kira suna cewa ku ro ki bukatunku sannan su zauna tare dama su ambaton Allah su lullube su da fukafukansu har zuwa sama, idan aka gama ambaton Allah aka watse Malaiku su ka ko ma sama sai Allah ya tambaye su dukda cewa ya san inda suka je (dan akambama ladam ma su ambaton Allah) sai yace musu daga ina kuke? Sukace daga wurim bayinka Adoron kasa suna tamaka tasbihi suna girmama ka suna gode maka kuma suna kambama ka sai Allah yace To sun taba gani na ne Malaiku suce aa ya Rabbi lallai basu taba ganinkaba Allah yace To ya kuke gani da sun taba gani na? sukace Ai da sun taba ganinka da sunfi haka yima ibada, kuma da sumfi haka ma godiya da kuma sun yawaita ma tasbihi Allah yace To wai me suke roko na ne sukace Aljannah suke rokonka ya Allah Allah yace to sun taba ganin Aljannar ne? sukace la wallahi ya rabbi basu taba gani ba Allah yace To da sun taba ganintafa? Malaiku sukace Lallai da sunganta da sun tsananta kwadayi akanta da sun tsananta nemanta da kuma sun kara girma ma kwadayinta. sai Allah yace To kuma akamme suke neman tsari na? Sukace Suna neman tsari ne daga Wuta Allah yc sun taba ganin Wutar ne? Suka ce la wallahi basu taba gani ba ya Allah Allah yc da sun taba gani fa? Malaku sukace Ai da sun taba ganin wuta da sun tsananta nisantarsa, da kuma sun tsananta tsoro! Sai Allah mai rahma dajin kai yace To ku musu albishir da cewa na gafarta musu, na ba su abinda suke ro ko na kuma tseratar dasu daga abinda suke tsoro sai Malaikun sukace To ammafa acikinsu akwai wani Mutum shi kam wuce wa kawai yazoyi saboda wata bukatarsa sai yadan tsaya.. Allah yace Na gafarta masa shi ma, dan wadan nan (ma su ambaton Allah) wasu Muta ne ne da duk wanda ya zauna dasu bazaiyi rashin rabo ba wato ya ci albarkacinsu. Allah karim! Yan uwan Eeman, shiyasa akodayaushe ake kwadaitar damu zama da Mutanen kirki masana addini dan baza ka taba raguwa da su ba sai dai kaita karuwa ga na ilimi ga kuma lada awurin Allah. Allah ma da kansa ya kwadaitar damu zama da irin wadannan saaliham bayi inda yake cewa KA HAKURTARDA KANKA ATARE DA MUTANENDA SUKE AMBATON ALLAH SAFIYA DA MARAICE SUNA NEMAN YARDAR ALLAH... Allah ya da tardamu ya ba mu hakuri da juriyar zama dasu, dan sai Munjure saboda Sheadanu dake ya wo su ma suna neman wanda ya shagala su kara shagaltar dashi su nisanta shi daga ambaton Allah. Waiyazubillah
Posted on: Mon, 21 Oct 2013 10:55:55 +0000

Trending Topics



style="margin-left:0px; min-height:30px;"> Suspender Man™ thanks Bojidar Marinov for pointing out that 1
14.1 ½ hh, 5 y.o Reg Riding Pony Gelding. A true show horse,
is month. Mom today
Prime Choice Auto Parts CAK650 Front Right Upper Control Arm

Recently Viewed Topics




© 2015